Burkina Faso

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Burkina

Masu zanga-zanga a kasar Burkina Faso
Masu zanga-zanga a kasar Burkina Faso AFP/AHMED OUOBA

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a kasar Burkina Faso bayan ‘Yan adawa sun kaddamar da kazamar zanga-zanga domin adawa da shirin tazarcen shugaba Blaise Compaore wanda ya kwashe shekaru 30 yana mulki a cikin kasar.

Talla

Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar bayan sun nufi ginin Majalisa a birnin Oougadougou.

Mutane kimanin Miliyan guda ne suka shiga zanga-zangar ta adawa da shugabancin Campaore.

Tuni gwamnatin kasar ta rufe makarantu da Jami’oi saboda fargabar barkewar zanga-zangar adawa da tazarcen Campoare a zaben 2015.

Shugaba Campaore yana neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ne domin samun damar sake tsayawa takarar shugaban kasa.

A shekara ta 1987 ne Campaore ya kwace mulkin kasar Burkina faso da karfi inda ya hambarar da gwamnatin Thomas Sankara tare da kashe shi

Kuma tun a lokacin har yanzu shi ne shugaban kasar Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.