Bakonmu a Yau

Alkasum Abdurrahman Masanin Siyasar Afrika

Sauti 03:18
Wani mai zanga-zanga dauke da wani allon da aka rubuta kalaman adawa da Shugaban Burkina Faso Blaise Compaore
Wani mai zanga-zanga dauke da wani allon da aka rubuta kalaman adawa da Shugaban Burkina Faso Blaise Compaore REUTERS/Joe Penney

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a kasar Burkina Faso bayan ‘Yan adawa sun kaddamar da kazamar zanga-zanga domin adawa da shirin tazarcen shugaba Blaise Compaore wanda ya kwashe shekaru 30 yana mulki a cikin kasar. Compaore yana son sauya kundin tsarin mulkin kasar ne don samun damar ci gaba da mulki a wa’adi na uku. Akan haka ne Nasirudden Muhammad ya tattauna da Alkasum Abdurrahman masanin siyasar Afrika.