Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane da dama a Kukawa

Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram Fuente: YouTube

Mayakan Boko Haram sun abkawa garin Kukawa a Jihar Borno inda suka kashe mutane da dama, kamar yadda mahukuntan garin suka tabbatar. ‘Yan sanda sun ce Mayakan sun bude wuta ne a wata kasuwar garin.

Talla

Kukawa da ke kusa da tabkin Chadi yana cikin garuruwan da ke fama da hare haren Mayakan Boko Haram

Shugaban karamar Hukumar garin na Kukawa Modu Musa yace Mayakan sun kai harin ne a ranar Litinin, kuma Jami’an tsaro ba su Ankara ba saboda matsalar layukan salula da aka lalata shekaru biyar da suka gabata.

Musa yace bayan Mayakan sun bude wuta sun kuma kona kasuwa da Ofishin ‘Yan sanda da gine ginen gwamnati.

Rahotanni sun ce sai daga bisani ne Jami’an tsaro suka yi kokarin tunkarar mayakan.

Wannan dai ke kara cusa shakku da alamar tambaya ga ‘Yan Najeriya akan ikirarin gwamnati na cim ma yarjejeniyar tagaita wuta da mayakan Boko Haram, musamman game da kubutar da ‘Yan matan garin Chibok da suka sace a tsakiyar watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.