Zambia

Michael Sata na Zambia ya rasu

Marigayi Shugaban Zambia Michael Sata
Marigayi Shugaban Zambia Michael Sata Reuters/Mike Segar

Rahotanni daga Zambia sun tabbatar da rasuwar Shugaban kasar Michael Sata mai shekaru 77 a birnin London inda ake kula da lafiyarsa. Kuma fadar shugaban kasar a birnin Lusaka ta tabbatar mutuwar Shugaban.

Talla

Amma Jaridu da dama a Zambia sun tabbatar da mutuwar shugaban.

An dade ana jita jitar rashin lafiyar Sata bayan dadewa ba a gan shi a bainar jama’a ba tun lokacin da ya dawo babban taron Majalisar Dinkin Duniya a watan jiya.

Masana siyasar Zambia sun fara fashin baki game wanda zai gaji shugaban.

A lokacin da zai tafi London neman magani, Shugaba Sata ya nada Ministan tsaro da Shari’a a matsayin wadanda zasu tafiyar da gwamnati.

Masana siyasar kasar suna ganin Mataimakinsa Guy Scott yana da wahala ya gaji Sata saboda iyayensa ba ‘Yan asalin Zambia ba ne.

TARIHIN SATA

Micheal Chilufya Sata a ranar 23 ga watan Satumba ne ya fara shugabancin Zambia karkashin tutar Jam’iyyar PF.

Sata ya rike mukamin Minista a zamanin shugaba Frederick Chiluba, kuma ya taba zama Gwamnan birnin Lusaka tare da zama Dan Majalisa.

Kafin zamansa Shugaban kasa ya taba zama babban dan adawa wanda ya kara da shugaba Levy Mwanawasa a zaben 2006, inda ya sha kaye a zaben.

Bayan mutuwar Mwanawasa, sata ya sake shan kaye a zaben shugaban kasa a karawar da suka yi da Rufiah Banda a 2008.

Amma a 2011 ne Sata ya doke Banda da gagarumin rinjayen a zaben shugaban kasa.
Michael Sata ya samu digirinsa na farko a ilimin Siyasa.

An haifi Sata ne a shekara ta 1937 a wani kauye da ake kira Mpika a arewacin Zambia, kuma ya taba aikin dan sanda.

Amma Sata ya mutu a yau 29 ga watan Oktoba a birnin London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.