Burkina Faso

Shugabannin Afrika na son dawwama a karagar mulki

Shugaba Blaise Campaore na Burkina Faso
Shugaba Blaise Campaore na Burkina Faso Reuters/Katrina Manson

Zanga-Zangar adawa da ake a kasar Burkina Faso kan shirin shugaba Blaise Compaore na sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da zama a karagar mulki ta dada fito da bukatar shugabanin Afrika na ci gaba dawwama a kan karagar mulki.

Talla

Yanzu haka shugabanin da suka kwashe sama da shekaru 15 a karagar mulki sun hada da Ismael Oumar Guelleh na Djibouti, wanda ya kwashe shekaru 16 yana shugabanci, sai Abdelaziz Bouteflika na Algeria wanda shi ma ya kwashe shekaru 16 yana shugabanci.

Baul Biya na Kmaaru wanda ke wa’adi na shida, ya kwashe shekaru 32 a karagar mulki. Idris Deby ma na Chadi ya kwashe shekaru 22 yana shugabanci.

Robert Mugabe na Zimbabwe ya shafe shekaru 32 a saman mulki.

Yanzu haka kuma ana zargin shugabanin kasashen Rwanda da Congo da Jamhuriyar Demokradiyar Congo na shirin sauya kundin kasashensu domin samun damar yin tazarce.

Blaise Campaore na Burkina Faso yana kokarin sauya kundin tsarin mulki ne domin samun damar zarcewa akan karagar mulki.

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a kasar Burkina Faso bayan ‘Yan adawa sun kaddamar da kazamar zanga-zanga domin adawa da shirin tazarcen Compaore wanda ya kwashe shekaru 30 yana mulki a cikin kasar.

Tuni gwamnatin kasar ta rufe makarantu da Jami’oi saboda fargabar barkewar zanga-zangar adawa da tazarcen Campoare a zaben 2015.

A shekara ta 1987 ne Campaore ya kwace mulkin kasar Burkina faso da karfi inda ya hambarar da gwamnatin Thomas Sankara tare da kashe shi.

Kuma tun a lokacin har yanzu shi ne shugaban kasar Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.