Cutar Ebola na raguwa a kasar Liberia

Alamar hukumar lafiya ta duniya, WHO
Alamar hukumar lafiya ta duniya, WHO

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tace ana samun raguwar mutanen da suke kamuwa da cutar Ebola a kasar Liberiya sai dai hukumar ta yi gargadin cewa har yanzu da sauran aiki a kokarin dakile cutar a kasar. A lokacin da yake yiwa maneman labari bayyani a geneva Mataimakin babban darakata hukumar Bruce Aylward yace wanna cigaba ba yana nufin an kawo karshan cutar ba, amma dai alamu ne na cewa an samu raguwar yaduwar cutar a liberia kuma da wanna za a iya kawo karshan cutar a kasar.Yace sai dai haka ba yana nufin mutane su saki jiki bane, a cewar shi dole a cigaba da taka tsantsan, hade da maida hankali wajen tsafta.Hukumar tace sabon adaddin mutane dake dauke da cutar a yanzu sun haura dubu 13, adaddin daya haura kididga da suka fitar a baya, kuma yawancinsu ‘yan asalin yammacin Afrika ne wadanda suka hada da kasar Guinea, Liberia, da Saliyo, inda cutar tafi tsanata a yanzu.A banagare guda kuma kasar Amurka ta kebe dakarunta da suka dawowa daga yankin Yammaci Africa, tsahon kwanaki 21 don kare kasar su daga cutar.Alyward yace yanzu babu mutum ko guda a kwance kan gadaje da ake kula da masu dauke da cutar a kasar, wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban Amurka Barak Obama, da kungiyar agaji ta Red Cross sun bada tabbacin samun cigaba a wajen yaki da cutar a kasar.