An nada Guy Scott a matsayin shugaban rikon kwaryan Zambia

Shugaban rikon kwaryan kasar Zambia, Guy Scott
Shugaban rikon kwaryan kasar Zambia, Guy Scott Wikimedia Commons

Majalisar zantarwa ta kasar Zambia ta baiwa Guy Scott rikon kwayan shugabancin kasar, sakamakon mutuwar tsohon shugaban kasar, Michael Sata, wanda ya rasu a birnin London.Guy Scott, zai kasance farin fatan na farko daya mulki wata kasa a nahiyar Afrika, karkashin mulkin demokradiyya.An haifi Dr. Guy Lindsay Scott a ranar 1 ga watan Yunin shekara ta 1944, a garin Livingston dake kasar zambia. Mahaifinshi, Alec Scott yazo garin ne a shekara ta 1927 yayinda mahaifitarsa, Grace Scott itama tayi hijara zuwa garin a shekara ta 1940sabon shugaban kasar dai ya kammala karatunsa na farko a kudancin kasar Rhodesia a wancan lokacin, wanda daga bisani ta koma Zimbabwe.Har ila yau Guy Scott yayi karatu a jami’ar Cambridge dake Birtaniyya, inda ya karbi digiri a fannin tattalin arziki.Mahaifinsa ne ya karfafa masa gwiwa wajan shiga harkar siyasa a kasar ta Zambia, bayan ya kasance mutum na farko daya samar da jaridun dake sukan mulkin mallakan a kasar.A shekara ta 1965 ne Guy Scott ya shiga cikin gwamnatin kasar inda ya fara aiki a matsayin mai tsare-tsare a ma’aikatar kudi ta kasar.A shekara ta 1991 ya wakilci mazabar Mpika a majalisar dokoki, karkashin jam’iyar MDD.Daga baya Guy Scott ya bar jam’iyar ta MDD inda ya koma jam’iyar PF, data bashi damar samun mukamin mataimakin shugaban kasa a shekara ta 2011.A jiya, bayan mutuwar tsohon shugaban kasar, Michaael sata, ya zamo farkon farin fatan da zai mulki wata kasa a nahiyar Afrika a mulkin demokradiyya.