Burkina Faso

'Yan adawa a Burkina Faso sun ce an yi juyin mulki a kasar

30 octobre : Les forces de l'ordre bloquent les manifestants à Ouagadougou.
30 octobre : Les forces de l'ordre bloquent les manifestants à Ouagadougou. Issouf Sanogo/AFP

Wani jigo a Jami’iyyar Hamayyar kasar Burkina Faso Benewende Sankara ya bayyana karbe harkokin gudanarwar Gwamnati da Sojin kasar suka yi juyin mulki ne. Sankara haka ma ya bayyana cewar batun dawowar tsohon shugaba Blaise Compaore a kan Karagar mulkin kasar ba mai yiyuwa ba ne

Talla

Jagoran ‘yan adawar Benewende Sankara, ya ce shugaba Blaise Compaore wanda ya jagoranci kasar na tsawon Shekaru 27 ya sake dawowa da wani salon yaudarar mutane.

Yace sun sha bayyanawa karara cewar ya kamata Compaore ya ajiye mulki amma ya ki.

A jiya Alhamis dai Blaise Compaore, daga wata Malabar da ya samu, ya bayyana kafa dokar ta-baci, bayan tashin hankalin da ya barke sakamakon boren da jama’a suka tayar.

Har yanzu dai babu tabbas akan wanda ke rike da Ragwamar mulkin kasar tsakanin Soji da Blaise Compaore shugaban kasar da a halin yanzu ke labe a wani lungu.

Ya zuwa dai an bayyana kisan akalla mutane 30 da jikkata wasu sama da 100 a tashin hankalin da ya barke a kasar da ke a yankin Nahiyar Afrka ta Yamma.

Can a babban birnin kasar Ouagadougou ma an bayyana yanda masu zanga-zangar suka kona Majalisar Dokokin kasar, abinda ba’a taba samu ba a baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.