Sudan

Wani Mutum ya kashe dogaran fadar Al Bashir 2

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir a Khartoum Fadar gwamnatin kasar.
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir a Khartoum Fadar gwamnatin kasar. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah

Wani Dan bindiga ya kashe sojoji biyu a fadar shugaban kasar Sudan tare da harbe kansa a lokaci da ya yi kokarin kutsa kai zuwa Ofishin Shugaba Omar al-Bashir. Fadar gwamnatin tace mutumin ya kwace bindigar daya daga cikin Jami’an tsaro ya harbe biyu daga cikinsu tare da harbe kansa bayan ya samu tsallakawa kofar shiga fadar Al bashir.

Talla

Kakakin Sojan Sudan yace, Maharin ya yi kokarin shiga fadar shugaban kasa ne dauke da Takobi kafin ya kwace bindiga.

Maharin da aka bayyana sunansa a matsayin Salah Kafi Quwa, ya fito ne daga Jihar Kordufan inda ‘Yan tawaye ke gwabza fada da gwamnatin Al Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI