'Yan Afrika sun fi mutuwa a Teku
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace ‘Yan asalin Afrika da yara kanana 372,000 ke nitsewa a cikin teku a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai. Binciken hukumar yace yada da wahala a samu Bature guda ya nitse a Teku.
Shugabar Hukumar Margareth Chan tace duk da kokarin rage mutuwar kananan yara a duniya, ana ci gaba da samun matsalar yaran da ke mutuwa a cikin teku.
Rahotan hukumar yace akan samu matsalar nitsewar yaran ne saboda akasarin su ba sa samun kula a cikin kwale kwalen.
Rahotan ya kuam ce yaran da ke kasa da shekaru 25 suka fi mutuwa a irin wanan yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu