Burkina Faso

An nada Zida a matsayin Firaministan Burkina

Henry Ye,tare da Kanal  Isaac Zida, à Ouagadougou
Henry Ye,tare da Kanal Isaac Zida, à Ouagadougou AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

An nada Kanal Isaac Zida a matsayin Firaministan kasar Burkina Faso wanda ya jagoranci gwamnati Soja bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore. Shugaban gwamnatin rikon kwarya Michel Kafando ne ya nada Zida wanda ya mika masa ragamar tafiyar da kasar.

Talla

An zabi Zida ne a mastayin Firaminista bayan amincewar ‘Yan siyasa da shugabannin Sojan kasar.

A ranar Talata ne aka rantsar da Kafando a matsayin shugaban rikon kwarya, domin jagorantar Burkina Faso har zuwa a gudanar da zaben shugaban kasa.

A ranar Juma’a ne Kafando zai karbi ragamar tafiyar da Burkina Faso daga hannun Kanal Zida.

Sauyin gwamnati da aka samu a Burkina Faso na zuwa ne kafin cikar wa’adin kungiyar Tarayyar Afrika, bayan gargadin kakabawa kasar takunkubi idan har sojoji ba su mika mulki ga Farar hula ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.