Afrika ta Kudu

Kotu ta amince a kalubalanci hukuncin Pistorius

Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu
Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko

Alkaliyar Kotun kasar Afrika ta kudu ta ba masu shigar da kara damar kalubalantar hukuncin daurin shekaru biyar da aka yanke wa Pistorius bayan sun ce an yi wa Dan tseren guragun sassauci ta la’akari da kisan budurwarsa da ya aikata.

Talla

Yanzu Pistorius na iya fuskantar daurin shekaru 15, idan har Kotun Koli ta tabbatar da laifin kisa akansa.

Masu gabatar da kara sun  kalubalanci sassaucin daurin shekaru 5 da kotun ta yi wa Oscar Pistorius bayan kama shi da laifin kisan budurwarsa.

Masu gabatar da karar dai na ganin Kotun ta yi wa dan tseren guragun sassauci da yawa, saboda yadda ya bindige budurwarsa.

A watan Oktoba ne kuma suka nemi izinin daukaka kara don kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.

Daga cikin lauyoyin da ke neman daukaka karar ya kalubalanci mai shari’a Masipa bayan ta yanke hukuncin tana mai fakewa da cewa Pistorius ya bindige budurwarsa ne ba da gangan ba.

Idan dai har mai shari’a ta amince da bukatar masu shigar da kara, za a ci gaba da Shari’ar Pistorius a kotun kolin Afrika ta kudu.

Tuni kuma Pistorius ya amsa cewa ya harbi budurwarsa har sau hudu a ban-dakin gidansa a ranar masoya da ake kira Valentine a shekarar 2013.

Wasu mutanen Afrika ta kudu sun bayyana cewa Kotun ta fifita rayuwar Oscer Pistorius fiye da rayuwar budurwar shi da aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.