Najeriya

Rabilu Musa Dan Ibro ya rasu

Rabilu Musa Dan Ibro
Rabilu Musa Dan Ibro facebook

A yau Safiyar Laraba Allah ya yi wa Fitattacen dan wasan barkwanci na Hausa Rabilu Musa Dan Ibro rasuwa, kuma ya rasu ne a gidansa da ke Dan Lasan a karamar hukumar Warawa a Jihar Kano. Dan Ibro ya shahara a Fina-finan ban-dariya na Hausa, kuma ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Talla

Dalhatu Musa Dakata da ke fitowa a cikin Fim din Dan Ibro kuma wanda ake kira Dandano ya tabbatarwa RFI Hausa da labarin rasuwar Dan Ibro.

A kwanan baya an ta yada jita jitar Ibro ya rasu, a lokacin Ibro ya fito a kafafen yada labarai yana godewa magoya bayansa saboda kauna da aka nuna masa da sakwanni sakamakon jin labarin mutuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.