Najeriya

PDP ta tabbatar da Jonathan a matsayin dan takara

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da matar sa Patience da kuma Gwamnan Bauchi Isa Yuguda ke amsa gaisuwa daga magoya bayansa a wajen taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da matar sa Patience da kuma Gwamnan Bauchi Isa Yuguda ke amsa gaisuwa daga magoya bayansa a wajen taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a Abuja. RFI hasau/kabir

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta tabbatar da takarar shugaba Goodluck Jonathan da Namadi Sambo a zaben shekara mai zuwa, tare da amincewa da Ahmed Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyar. A taron, Jam’iyar ta ta sha alwashin gudanar da mulki na gari domin magance kalubalen da ke fuskantar kasar.

Talla

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawalin yaki da matsalar cin hanci da rashawa da kuma matsalar tsaro da ke barazana ga ci gaban kasar.

Taron PDP da aka gudanar a Abuja na zuwa a yayin da babbar Jam’iyyar Adawa ta APC ke taronta a birnin Lagos domin tsayar da Dantaka da zai fafata da Jonathan a zaben 2015.

Rahoton taron PDP a Abuja

Wakilan APC kimanin 8,000 ne zasu zabi Dan takara tsakanin Tsohon Shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari da Tsohon Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Imo Rochas Okorocha da Mawallafin Jaridar Leadership Sam Nda Isaiah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.