Najeriya

APC ta zabi Osibanjo a matsayin mataimakin Buhari

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde

Jam’iyyar adawa ta APC a Najeriya ta zabi tsohon Atoni Janar na Jihar Lagos Farfesa Yomi Osibanjo a matsayin wanda zai marawa Janar Muahmmadu Buhari baya a zaben shekara mai zuwa.

Talla

Batun wanda zai yi wa Buhari mataimaki ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin jiga-jigan jam’iyyar domin an samu rarrabuwar kawuna kan wanda ya dace tsakanin tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da Gwamna mai ci Babatunde Fashola da Gwamnan Edo Adams Oshimhole da takwaransa na Rivers Rotimi Amaechi.

Gobe ne wa’adin da hukumar zabe ta gindaya na mika sunan dan takara da mataimakin sa zai cika.

Tsohon Shugaban kasar Janar Muhammadu Buhari zai fafata ne da Shugaba mai ci Goodluck Jonathan.

Yanzu haka kuma Kotun Kolin Najeriya ta janye karar da aka shigar domin hana shugaba Goodluck Jonathan takarar zaben shekara mai zuwa. Sai dai wata kungiyar da ta kira kanta Northern Initiative ta bukaci shugaban ya sake tunani kan takararsa, suna masu kalubalantar cancantarsa bisa tsarin doka.

Jam’iyyar PDP mai mulki ta tabbatar da Goodluck Jonathan a matsayin dan takararta ba hammaya.

Amma Shugaban Kungiyar Northern Initiative Bala Alaramma yace ‘Yan Najeriya sun san ana tsayawa takara ne sau biyu tare da rantsar da mutum sau biyu.

Masu fashin bakin siyasa a Najeriya suna ganin Zaben 2015 zai kasance mafi zafi a tarihin siyasar kasar.

Hukumar zabe a Najeriya tace har sai an sauya dokar zaben kasar kafin dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya sa suka tserewa gidajensu su iya shiga babban zaben 2015 da za a gudanar a watan Fabrairu.

Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ya bukaci hukumar zaben kasar ta dauki matakan da suka dace wajen ganin mutanen da suka tserewa matsugunansu sakamakon rikicin Boko Haram sun yi zaben shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.