Ebola

Ana shiga gida gida don gano masu Ebola a Saliyo

Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar Ebola a Liberia
Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar Ebola a Liberia © RFI/Sébastien Nemeth

Gwamnatin Kasar Saliyo ta kaddamar da aikin shiga gida gida don gano masu dauke da cutar Ebola a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar. Shugaba Ernest Bai Karoma ya yi jawabi ga al’ummar kasar inda ya dakatar da tafiye tafiye a tsakanin yankunan kasar da kuma bukatar ganin an bai wa jami’an hadin kai wajen gudanar da aikinsu.

Talla

Shugaban yace za a bar Kiristoci su je mujami’a ranar kirsimeti amma daga nan kowa gida zai koma babu shagulgula.

Hukumar Lafiya ta duniya WHO tace kimanin mutane 6,900 suka mutu sakamakon Ebola a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.