Zambia

Shugaban rikon Zambia ya ki sauka

Shugaban rikon kwaryan kasar Zambia, Guy Scott a taron Afrika da Obama a Amurka
Shugaban rikon kwaryan kasar Zambia, Guy Scott a taron Afrika da Obama a Amurka REUTERS/Larry Downing

Shugaban kasar Zambia na riko, Guy Scott ya sa kafa ya shure kuri’ar rashin amincewa da shi da wakilan majalisar zartaswan kasar suka gabatar ma sa. Wakilan majalisar Zartarwan kasar 14 daga cikin 17 ne suka kira taron gaggawa inda suka zartas da bukatar shugaban kasar na riko ya sauka.

Talla

Rikicin cikin gida tsakanin wakilan majalisar kasar da sugaban kasar wanda shi ne farar fata dan Afrika na farko da ke mulkin kasar cikin shekaru 20 da suka gabata, na fitowa sarari ne gabanin babban zaben kasar da ke tafe cikin watan gobe.

Sai dai kuma a nashi bangaren Shugaba Guy Scott ya ce shi ne kawai ke da izinin ya kira taron wakilan majalisar kasar amma ba wani ba, kuma taron da suka yi inda suka zartas da ya sauka tamkar cin amanan kasa suka yi.

Cikin jamiyyar da ke mulki ne dai aka sami baraka inda suke bukatar a nemo dan takara da ya dace a zaba, yayin da wasu ke ganin a mika mulkin ga wani dan uwan marigayi shugaban kasar Michael Sata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.