Gambia

An cafke mutane da dama kan zargin juyin mulki a Gambia

Shugaban kasar  Gambia Yahyah Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahyah Jammeh AFP PHOTO / SEYLLOU

An cafke mutane da dama, da ake zargi suna da hannu a yunkurin jurin juyin mulkin da aka yi a kasar Gambia, lokacin da shugaban kasa Yahya Jammeh ke ziyara a birnin Dubai, wanda kuma ya dora alhakin harin kan ‘yan kasashen waje da bai bayyana sunayen su ba.

Talla

Wata majiya daga bangaren leken asirin kasar, tace an kuma sami makamai masu tarin yawa da abubuwa masu fashewa, da aka so yin amfani dasu a yunkurin juyin mulkin, na daren ranar Talata.

Yanzu haka dai ana tsare da wadanda ake zargi da hannu a lamarin, a wasu gidajen da ke Banjul fadar gwamnatin kasar.

Yahya Jammeh ya kwashe shekaru 20 yana shugabanci a Gambia, kuma ya zargi kasashen waje da ke adawa da gwamnatinsa da ke son kawo karshen mulkinsa a Gambia

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.