Saliyo

Ebola: Likitan Italiya ya warke

© Reuters

Wani likitan kasar Italiya da ya kamu da cutar Ebola ya sami sauki, bayan an kula da lafiyarsa da wasu magunguna gwaji a cibiyar Spallanzani da ke birnin Rome inda aka killace shi. Amma ba a bayyana sunanshi ba, bayan da ya kamu da cutar a kasar Saliyo a cikin watan Nuwamba.

Talla

Wata ma’aikaciyar jinya ‘yar kasar Britaniya ma ta sami sauki daga cutar ta Ebola, bayan da aka yi gwajin magani a kanta, tare da sinadarin jinin wani da ya warke daga cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.