Najeriya

Boko Haram ta sace Matasa 40 a Malari

Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM

Mayakan Boko Haram sun sace wasu matasa kimanin su 40 a kauyen Malari da ke cikin Jihar Borno a arewacin Najeriya. Wasu mazauna garin sun tabbatarwa kamfanin Dillacin labaran Faransa a yau Assabar cewa a jajibirin sabuwar shekara ne da dare wasu ‘Yan bindiga da ake zargin ‘Yan Boko Haram haram ne suka sace matasan masu shekaru 10 zuwa 23 kuma sun gudu da su zuwa dajin Sambisa.

Talla

Labarin sace matasan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wasu mutanen kyauyen na Malari sun tsere zuwa birnin Maiduguri ranar Juma'a.

Mazauna garin sun ce ‘Yan bindigar sun tara mutanen garin a harabar gidan Mai gari suna wa’azi bayan sun shigo kauyen cikin mota a-kori-kura dauke da bindigogi kafin sace yaran.

Kauyen Malari dai na kusa ne da Dajin Sambisa dab da garin Gwoza da Mayakan Boko Haram suka kwace a watan yunin 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.