Afrika ta Tsakiya

An tsawaita gwamnatin rikon kwarya a Afrika ta tsakiya

Shugabar Africa ta Tsakiya Catherine Samba-Panza
Shugabar Africa ta Tsakiya Catherine Samba-Panza AFP PHOTO / Eric FEFERBERG

An tsawaita wa’adin gwamnatin rikon kwarya ta jamhuriyar Afirka ta tsakiya har na watanni shida, inda ake fatar gwamnatin za ta shirya zabe da kuma mika mulki ga hannun farar hula a karshen watan Agustan wannan shekara. Babban mai shiga tsakanin na kasashen yankin tsakiyar Afirka kuma shugaban Congo Brazaville Denis Sasso Nguesso, shi ne ya tabbatar da hakan a wata wasika da ya aike wa shugabannin gwamnatin rikon kwaryar da suka fito daga bangarorin uku da ke hannu a rikicin kasar.