Ebola

Za a daina yi wa ‘Yan Mali binciken kwakwab a Amurka

Jami'an Kiwon lafiya na tantance Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon a lokacin da ya ke ziyara kasashen da ke fama da Ebola a yammacin Afrika
Jami'an Kiwon lafiya na tantance Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon a lokacin da ya ke ziyara kasashen da ke fama da Ebola a yammacin Afrika REUTERS/James Giahyue

Gwamnatin Amurka na shirin cire kasar Mali daga cikin kasashen da ake yi wa fasinjojinsu binciken kwakwab inda suka sauka a filin jiragen saman Amurka saboda bullar Ebola a kasar. A yau talata, kwanaki 42 ke nan ba tare da an samu karuwa wani mutum da ya kamu da wannan cuta ba a Mali.

Talla

Hakan ke tabbatar da cewa an samu nasarar kange annobar daga yaduwa a kasar Mali, kuma daga nan ne Amurka za ta cire sunan kasar Mali daga cikin wadanda ake sanya wa ido.

Cutar Ebola ta kashe mutane shida a kasar Mali bayan an shigo da cutar daga Guinea.

Adadin mtane kimanin 8,153 Ebola ta kashe a kasashen yammacin Afrika yawanci a Saliyo da Liberia da Guinea inda cutar ta fi yaduwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.