Mali-Libya

Mali ta nemi a tura Sojoji a Libya

Mayakan sa-kai  à Kikla kasar Libya
Mayakan sa-kai à Kikla kasar Libya AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA

Kasar Mali ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta tura sojojinta domin shawo kan rikicin da ya addabi Libya da ke neman mamaye Yankin Sahel. Ministan harkokin wajen kasar Abdoulaye Diop ne ya bayyana haka yayin da ya ke jawabi a kwamitin Sulhu a madadin kasashe biyar da suka fito daga Yankin Sahel.

Talla

Diop yace duk abin da ke faruwa yanzu haka a Libya na da nasaba da kasarsa ta Mali, da kuma barazanar ayyukan kungiyar ISIS da Al Shebaab da kuma kungiyar Boko Haram wadanda ke neman lalata Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.