Najeriya

Shell ya amince ya biya mutanen Bodo diyya

Mutanen Naija Delta kusa da wani bahon danyen mai.
Mutanen Naija Delta kusa da wani bahon danyen mai. REUTERS/Akintunde Akinleye

Kamfanin hakar mai na Shell ya amince ya biya masuntan yankin Naija Delta kimanin 15,600 kudaden diyyar kudi kan gurbata ma su muhalli bayan shafe shekaru kusan uku suna kalubalantar Kamfanin a kotu.

Talla

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana amincewarta ga matakin Kamfanin Shell na biyan al’ummar Kauyen Bodo a Jihar Rivers da ke Najeriya diyyar Dala miliyan 55 kan gurbata mu su muhalli, tana mai cewa wannan gagarumar nasara ce ga kamfanin.

Audrey Gaughran, Daraktan da ke kula da harkokin kasashen duniya na kungiyar ya bayyana diyyar a matsayin wani abin da zai farantawa al’ummar Bodo da aka gurbata wa muhalli da kuma hana su samun gudanar da harkokin su na yau da kullum.

A shekarar 2008 ne kamfanin na Shell ya zubar da man da yawan sa ya kai ganga 4,000 abin da ya gurbata Yankin da kuma kashe kifin da mutanen wurin suka dogara da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.