Afrika ta Tsakiya

Wani Kwamandan ‘Yan tawaye ya mika kansa a Afrika ta tsakiya

Caesar Acellam daya daga cikin kwamandojin Lords Resistance Army
Caesar Acellam daya daga cikin kwamandojin Lords Resistance Army

Wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin kwamandan kungiyar ‘Yan Tawayen Lords Resistance Army da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa ga sojojin Amurka da takwarorinsu n a Afirka da ke farautar ‘Yan tawayen a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki ta bayyana cewar jami’anta na kokarin tantancewa ko mutumin da ya bayyana kan sa a matsayin Dominic Ongwen shi ne wanda ake nema.

Talla

Jami’ar tace in dai an tabbatar da cewar shi ne to matakin da ya dauka zai raunana kungiyar.

Majalisar Dinkin Duniya tace Kungiyar ‘Yan tawayen LRA ta kashe mutane sama da dubu dari tare da sace yara kanana sama da dubu sittin a shekaru uku da kungiyar ta kwashe tana ta’asa a Afrika ta tsakiya.

Kwamandan mai suna Dominic Ongwen yanzu haka yana hannun Jami’an Amurka a Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.