Masar

21 ga watan Afrilu za a yi Shari’ar Morsi a Masar

Magoya bayan Muhammad Morsi a Masar
Magoya bayan Muhammad Morsi a Masar AFP PHOTO/OZAN KOSE

A ranar 21 ga watan Afrilu mai zuwa ne kotu a kasar Masar za ta yanke wa tsohon shugaban kasar Mohammad Morsi da kuma wasu magoya bayansa 14 da ake zargi da tunzura jama’a domin yin zanga-zanga hukunci.

Talla

Hukuncin zai kasance na farko a jerin zarge-zargen da hukumomin kasar ke yi Morsi tun bayan da aka tunbuke shi daga karagar mulki cikin watan Yulin shekara ta 2013.

Za a yi Morsi shari’a ne tare da manyan shugabannin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi.

Kotun Masar na tuhumar Morsi da lafin cin amanar kasa musamman kan batun tserewar ‘yan gidan yari.

Tun hambarar da gwamnatin Morsi, an yanke wa daruruwan magoya bayansa hukuncin dauri da kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.