Najeriya

Boko Haram ta kona garuruwa 16 a Borno

Garin Baga da mayakan boko haram suka kona
Garin Baga da mayakan boko haram suka kona

Garuruwa da kauyuka akalla 16 Mayakan Boko Haram suka kona a Jihar Borno yankin arewa maso gabacin Najeriya bayan sun karbe barikin Sojoji a Baga. Musa Bukar a karamar hukumar Kukawa ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa Boko Haram ta kwace garuruwa da dama.

Talla

Bukar yace Boko Haram ta kona garuruwa 16 kurmus da suka hada da Baga da Doron Baga da Mile 4 da Mile 3 da Bunduram.

Rahotanni sun ce daruruwan Mutanen garuruwan sun gudu yayin da wasu suka makale a tabkin Chadi.

A ranar Assabar ne Mayakan Boko Haram suka karbe Baga da hedikwatar Sojojin hadin guiwa na Chadi da Nijar da Najeriya.

Yanzu Boko Haram ta kwace garuruwan Najeriya da ke kan iyaka da kasashen Kamaru da Najeriya da Nijar da Kamaru.

A cikin makon nan ne Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya aiko da wani sabon sakon Bidiyo zuwa ga Shugaban Kamaru Paul Biya yana yi masa gargadi da wa’azi da kuma mutanen kasar akan su yi watsi da tafarkin dimokuradiya su rungumi Shari’ar musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.