Somaliya

Kungiyar al-shebab ta Somaliya na dada samun rauni

REUTERS/Feisal Omar

Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta bayyana cewa farmakin da Dakarunta, da na Somaliya ke kaddamarwa akan kungiyar al-shebab, na cigaba da raunata kungiyar ta al-shebab a kasar ta Somalia

Talla

Tun da dadewa ne dai kungiyar Alshabab da ke tada Kayar baya a Somalia, ta fara rauni, bayan ‘yan lokutan da ta dauka tana cin Karenta ba babbaka a birnin Mogadishu da kudancin Somalia yayin da aka fatattaketa daga yankunan daga bisani a shekara ta 2011.

Duk da haka, kungiyar na cigaba da kai hari a fakaice yayin da a ranar laraba aka zargeta da kaddamar da wani harin Bam da ya jikkata wani malamin jami’a.

A dayan bangaren kuwa, tun a Bara ne Dakarun sojin tarayyar Afrika, suka yi nasarar kwace wasu daga cikin yankunan da al-shebab ta mallake bayan dauki ba dadi tsakanin soji, da ‘ya’yan kungiyar, kamar yadda Maman Sadkou jakadan kungiyar tarayyar Afruka ya bayyana, bayan da ya kara cewa sojin sun kwace kashi 85 cikin 100 na wuraren da kungiyar al-shebab ta mallake a farko.

Jakadan dai ya ki sanar da shirinsu na harin da soji za su kai wa al-shebab nan gaba, sai dai ya tabbatar da cewa, suna kan gudanar da tattaunawa yadda ya kamata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.