Gambia

Shugaban Gambia ya nemi afuwar Birtaniya

Shugaban kasar  Gambia Yahyah Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahyah Jammeh RFI/Pierre René-Worms

Shugaban Kasar Gambia Yahya Jammeh ya nemi afuwar Birtaniya kan zargin da ya yi ma ta cewar akwai ‘yan kasar ta cikin wadanda suka yi yunkurin yi masa juyin mulki. A jawabin da ya yi wa sojojin kasar, shugaba Jammeh yace babu wata shaida da ke nuna cewar akwai hannun Birtaniya a yunkurin sakamakon bayanan da suka samu saboda haka ya nemi gafarar kasar.

Talla

Shugaban ya kuma gargadi ‘yan adawar cewar zai murkushe ma su tayar da hankali a cikin kasar.

Jami’an tsaron Amurka sun cafke mutane biyu ‘yan asalin kasar Gambia kuma Amurkawa bayan sun dawo daga Gambia inda ake zargin sun tafi kasar ne domin kitsa juyin mulkin da aka murkushe a ranar 30 ga watan Disemba.

Bangaren shari’ar Amurka ya bayyana sunayen mutanen a matsayin Papa Faal da Cherno Njie mazauna Amurka.

Yahaya Jammeh ya kwashe tsawon shekaru 20 yana shugabanci a Gambia kuma an yi yunkurin kifar da gwamnatinsa ne a lokacin da ya ke ziyara a Dubai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.