Kamaru

Sojojin Kamaru sun kashe ‘Yan Boko Haram 143

Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya
Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO/REINNIER KAZE

Gwamnatin kasar Kamaru tace Sojojinta sun kashe Mayakan kungiyar Boko Haram 143 bayan sun kai hari a wani barikin Soji a garin Kolafata da ke arewacin kasar. Akwai Sojan Kamaru da aka kashe a musayar wutar da sojojin suka yi da mayakan.

Talla

Kakakin gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma ne ya tabbatar da mutuwar Mayakan a wata sanarwa da ya bayar a kafofin yada labaran Kamaru.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Mayakan na Najeriya suka kaddamar da farmaki a kan iyakokin kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.

Tchiroma yace ‘Yan Boko Haram sun tsere bayan shafe sa’o’I sama da biyar Sojojin Kamaru na musayar wuta da su.

Shugaban Boko Haram ya fito a wani bidiyo a makon jiya yana yin gargadi ga gwamnatin Kamaru.

Tuni Kamaru ta baza Sojoji domin fatattakar Boko Haram a arewa mai nisa da mayakan ke yi wa barazana.

Boko Haram sun kutsa kai kauyukan Kamaru da suka hada da Makari da Amchide da Limani inda suke kashe na kashewa tare da sace abinci da dukiyar jama’a.

Kamaru ta yi amfani da jiragen yaki domin kai hari kan  Boko Haram da ke ci gaba da tabka ta’asa a kauyukan da ke kan iyakan kasar da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.