Kamaru-Najeriya

Boko Haram: Kamaru ta jinjina wa Sojojinta

Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya
Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya Reinnier KAZE / AFP

Rundunar tsaron kasar Kamaru ta jinjinawa dakarun kasar sakamakon nasarar da suka samu wajen murkushe mayakan Boko Haram da suka kai hari akan wani barikin sojin kasar. Amma Kakakin rundunar sojan kasar ta Kamaru Kanar Didier Badjeck, ya ce akwai bukatar sauran kasashen duniya su taimaka domin murkushe Boko Haram.

Talla

Sojojin sun ce duk da cewa suna samun nasara akan Boko Haram amma ya dace kasashen duniya su shigo domin kawo karshen ayyukan Mayakan.

Kanal Badjeck ya amsa cewa Sojojin Kamaru ne kadai ke farautar Boko Haram ba tare da Sojin Najeriya ba a garuruwan da ke kan iyakar kasashen.

Badjeck yace akwai bukatar a dauki matakai domin runguza kungiyar Boko Haram tun daga tushenta, tare da kaddamar da fada da ita a duk inda aka ga alamunta.

Sojojin na Kamaru sun ce ya kamata a tafiyar da aiki na hadin guiwa tsakanin kasashe, domin hakan zai sa a yi wa kungiyar da mayakanta kofar-rago, yayin da a hannu daya za a dauki matakan hana su samun makamai da kudaden tafiyar da ayyukansu.

Kamaru ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta shigo da Sojojinta kamar yadda ta faru a Mali da yankin Sahel.

Kanal Badjeck yace sun tsara yadda za su shiga dajin Sambisa saboda Sojojin Najeriya sun kasa korar Boko Haram a wasu yankunan da suka kwace.

A makon jiya Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani Bidiyo yana yin gargadi ga Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.