Uganda

Uganda za ta mika Ongwen ga ICC

Dominic Ongwen Kwamandan 'Yan tawayen Lord Army na Uganda
Dominic Ongwen Kwamandan 'Yan tawayen Lord Army na Uganda AFP PHOTO / INTERPOL

Rundunar Sojin kasar Uganda tace za ta mika kwamandan ‘Yan Tawayen Lords Resistances Army Dominic Ongwen zuwa ga kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC domin fuskantar shari’ar laifufukan yaki da cin zarafin Bil adama. Mai Magana da yawun Sojin kasar Paddy Akunda yace sun yanke hukuncin mika kwamandan kotun duniya sabanin rade-radin da ake cewar a kasar za a yi ma sa shari’a.

Talla

Jami’in yace hukumomin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ne za su mika Ongwen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.