Algeria

Algeria ta gano gawar Bafaranshen da aka kashe

Hervé Gourdel, Bafaranshen da aka kashe a Algeria
Hervé Gourdel, Bafaranshen da aka kashe a Algeria © Facebook/ Capture d'écran

Majiyoyin tsaro a Algeria sun ce an gano gangar jikin Herve Gourdel Bafaranshen da aka fillewa kai cikin watan satumbar bara a cikin kasar. Bayanai sun ce an gano gawar Gourdel ne a binne amma ba kai a kusa da garin Akbil inda ‘an bindiga suka sace shi a lokacin da ya ke yawon buda ido a cikin kasar Algeria.

Talla

Rundunar Sojin Algeria ta baza Sojoji ne 3,000 domin gano gawar Bafaranshen.

Yanzu haka mutane 15 ake zargi da fille kan Bafaranshen da aka sace ranar 21 ga watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.