Najeriya

Shugaban Najeriya Jonathan ya kai ziyara a Maiduguri

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara Maiduguri babban birnin Jihar Borno mai fama da hare haren Mayakan Boko Haram a Najeriya. Gwamman Jihar Borno Kashim Shettima ne ya tarbi Jonathan bayan ya isa Maiduguri da misalin karfe uku na rana a yau Alhamis.

Talla

Shugaba Jonathan ya shiga Borno ne tare da rakiyar babban kwamandan askarawan Najeriya Alex Badeh da mai ba shi shawara kan harakokin tsaro da kuma Sojoji kusan 200.

Tun 2013, Wannan ne karon farko da Jonathan ya kai ziyara Maiduguri duk da dinbim hasarar rayukan mutane da aka samu a yankin da kuma ‘yan matan Makarantar garin Chibok da aka sace su 276.

Wannan na zuwa ne a yayin da manyan Kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda biyu na dunya suka nuna hutunan da ke tabbatar da barnar da Boko Haram ta yi a garin Baga da Doron Baga da ke cikin Jihar Borno.

Hotunan da Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty da Human Right Watch suka dauka a tauraron dan adam bayan Boko Haram ta kai hare hare a Baga da Doron Baga sun tabbatar da cewa mutane da dama ne aka kashe tare da kona gidaje da dama.

Wasu na danganta cewa ziyarar tana da nasaba da Siyasa saboda Shugaban yana neman ci gaba da mulki a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.