Sudan ta Kudu

Yaki na iya sa makwabtan Sudan ta kudu fuskantar hasara

Turkish Kurds watch over the Syrian town of Kobani as they stand on top of a hill near Mursitpinar border crossing in the southeastern Turkish town of Suruc in Sanliurfa province October 11, 2014.
Turkish Kurds watch over the Syrian town of Kobani as they stand on top of a hill near Mursitpinar border crossing in the southeastern Turkish town of Suruc in Sanliurfa province October 11, 2014. Reuters/路透社

Wani Rahoto da aka fitar na cewar kasashen da ke makobtaka da kasar Sudan ta kudu, na iya hasarar Dalar Amurka biliyan 53, sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi

Talla

Rahoton ya ce kasashen da hasarar ka iya shafa sun hada da Sudan da Habasha ko Ethophia sai Kenya da Uganda kazalika da Tanzania.

Wannan na kumshe ne a cikin wani rahoto da aka fitar a ranar laraba, rahoton kuma ya kara da cewar hasarar makudan kudaden, za ta samesu ne, matukar rikicin kasar Sudan ta kudu ya tsawaita zuwa shekaru biyar.

Kasashen dai na ci gaba da dawainiya da ‘yan gudun hijara da yawansu ke karuwa a kai a kai, kuma suke samar masu da ingantaccen tsaro.

A dayan bangaren kuwa, wata cibiyar da ke bincike kan al’amurran tattalin arziki a birnin Landan, na Birtaniya, ta bayyana cewar tattalin arzikin sudan ta kudu ya ragu da kashi 15 cikin 100 a Shekarar Bara, sakamakon yakin basasa a kasar, da ya yi sanadiyar rayukan mutane 10,000 baya ga tauye yawan man fetir da kasar ke fitarwa.

Lura da hasasar mutane, da tawayar tattalin arziki, rahoton ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Duniya su gaggauta kai dauki domin kawo karshen rikicin sudan ta kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.