Kenya-Afrika ta Kudu

Wasu Jaridun Afrika sun nemi afuwar Musulmi

AFP/Bulent Kilic

Wasu Jaridun Afrika guda biyu da ake bugawa a kasashen Kenya da Afrika ta kudu sun nemi afuwar al’ummar musulmi game da zanen mujallar Faransa Charlie Hebdo da suka wallafa wanda ya ci zarafin musulmi. Jaridar Star ta Kenya da Jaridar the Citizen ta Afrika ta kudu ne suka nemi afuwar bayan sun yi nadama da abin da suke ganin cin zarafin muslmi ne.

Talla

Jaridun sun amsa cewa sun yi kuskure bayan dinbim musulmi da ke karatun Jaridun sun nuna bacin ransu tare da barazanar kauracewa jaridun saboda rashin sanin darajar addininsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.