Kamaru-Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kame mutane 60 a Kamaru

Askari wa Cameroon tarehe 17 Juni mwaka 2014, wanapiga doria katika mji wa mpakani wa Amchide, kaskazini ya mwa nchi, mji ambao unakabiliwa na mauaji yanayoendeshwa na Boko Haram.
Askari wa Cameroon tarehe 17 Juni mwaka 2014, wanapiga doria katika mji wa mpakani wa Amchide, kaskazini ya mwa nchi, mji ambao unakabiliwa na mauaji yanayoendeshwa na Boko Haram. Reinnier KAZE / AFP

Mayakan kungiyar Boko Haram a tarayyar Najeriya da suka fadada ayyukansu zuwa wasu sassan kasar Kamaru, sun kame akalla mutane 60 a wani mummunan harin da suka kai a yankin Arewacin kasar

Talla

Jami’an ‘yan sandan kasar ta Kamaru sun kuma tabbatar da kisan wasu mutane da dama sakamakon mummunan harin da aka ce ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram sun kai a yankin Arewacin kasar ta Kamaru.

Akasarin wadanda aka kama dai inji Kamfanin dillancin labarai na AFP Mata ne da kananan Yara.

Sai dai akwai labarin da ke cewar Rundunar Sojin kasar Kamaru da a halin yanzu ke shirin soma samun goyon bayan na kasar Chadi, sun kaddamar da kai hare-hare ga ‘ya’yan kungiyar bayan da ‘yan Boko Haram din suka yi garkuwa da mutanen 60.

Yanzu haka dai an ce Sojin Najeriya da na Chadi, na can suna kokarin sake karbe birnin Baga da ke da makwabtaka da Tafkin Chadi.

A kwanan nan dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty international, ta bayyana cewar kungiyar ta Boko Haram ta kashe akalla mutane farraen Hula 2000 a wani harin baya-bayan nan da suka kai, amma Dakarun Najeriya sun musanta hakan suna cewar mutanen da aka kashe basu haura 150 ba.

Amma Amnesty ta gabatar da shaidu na Hotunan da suka sama daga Tauraron dan Adam da ya nuna akalla gidaje sama da 3,700 da suka lalata a Baga da kuma Doron Baga.

Dakarun kasar Chadi 400 da aka tura domin taimakawa na Kamaru sun isa a kasar ta Kamaru ta bangaren yankin da ya hada iyakokin kasashen biyu na Kousseri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.