Zambia

Ana zaben shugaban kasa a Zambia

Magoya bayan Jam'iyyar PF a kasar Zambia
Magoya bayan Jam'iyyar PF a kasar Zambia REUTERS/Rogan Ward

A kasar Zambia an fara jefa kuri’ar zaben shugaban kasa a yau Talata tsakanin ‘yan takara guda biyu Ministan tsaro Edger Lungu na Jam’iyyar PF mai mulki da kuma Hakainde Hichelima na jam’iyyar adawa ta UNPND. Al’ummar kasar zasu zabi sabon shugaba ne bayan rasuwar Michael Sata.

Talla

Da misalin karfe shida na safe ne agogon kasar, karfe hudu agogon GMT aka bude runfunanr zabe a sassan kasar ta Zambia.

Duk dai wanda ya lashe zaben shi zai iyar da ragowar watanni 19 da suka ragewa marigayi Michael Sata wanda ya rasu a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Akwai batun tsarin haraji da jam’iyyun siyasar biyu ke jayayya akai, inda Jam’iyya mai mulki ta fito da sabon tsarin biyan haraji a watan Janairu yayin da kuma Hichelima ya yi alkawalin yin watsi da tsarin idan aka zabe shi.

Lungu lauya ne yayin da kuma Hichelima dan kasuwa, amma masu sharhi game da siyasar kasar Zambia na ganin ba za a iya cewa ga wanda zai lashe zaben ba

Mutane sama da miliyan 5 ke da ‘yancin kada kuri’ar zaben a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.