Najeriya

Boko Haram: MDD ta bukaci a kafa rundunar Afrika

Sojojin Kamaru a Dabanga, yankin arewa mai nisa da ke fuskantar barazanar Mayakan Boko Haram na Najeriya
Sojojin Kamaru a Dabanga, yankin arewa mai nisa da ke fuskantar barazanar Mayakan Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen Yammacin Afirka da tsakiya su gaggauta kafa runduna mai karfi da za ta murkushe kungiyar Boko Haram da ke cigaba da zama barazana ga Yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi allawadai da ayyukan Boko Haram da ke ci gaba da amfani da yara kanana a matsayin ‘yan kunar bakin wake tare da yin garkuwa da mata da yara.

Talla

Majalisar ta bukaci kasashen da ke makwabtaka da Najeriya su kafa rundunnar hadin guiwa domin aikin yaki da Boko Haram kamar yadda suka amince tun bara.

Tuni kasar Chadi tace za ta aika da dakaru 400 zuwa arewacin Kamaru domin yaki da Boko Haram kafin kafa runduna da za ta kunshi Sojojin Kamaru da Chadi da Benin da Nijar da Najeriya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen su amince da tsarin musayar bayanan tsaro na sirri a tsakaninsu domin kawo karshen barazanar Boko Haram a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.