Najeriya

Mun kwashi ganimar makamai a Baga- Boko Haram

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau AFP

Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a cikin wani sabon sakon bidiyo yana ikirarin daukar alhakin kai mummunn hari a garin Baga da Doron Baga a Jihar Borno da ke arewa maso gabacin Najeriya.

Talla

A cikin sakon bidiyon mai tsawon kusan minti 36 Shekau ya yi barazanar kaddamar da hare hare a Nijar da Kamaru da Chadi da ke makwabtaka da Najeriya.

Shekau ya kira shugaban Shugaban Nijar Mahamadou Issofou da Paul Biya na Kamaru da Idris Deby na Chadi.

Shugaban na Boko Haram ya gargadi Shugaban Nijar akan ziyarar da ya kai Faransa bayan harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo da ta ci zarafin musulmi.

Bidiyon ya nuna tarin makamai da Mayakan na Boko Haram suka ce sun samu a Barikin Sojoji da ke Mile 4 a garin Baga, Kuma kungiyar tace za ta yi amfani da Makaman da suka hada da bindiga kirar AK47 domin kai hare hare.

A cikin Bidiyon Shekau ya ce Najeriya ta shiga uku tare da kona tutar kasar.

Daruruwan mutane ne dai Mayakan na Boko Haram suka kashe a mummunan harin da suka kai a Baga da Doron Baga.

Tuni Shekau ya yi ikirarin kafa daular Musulunci a wasu garuruwan da mayakansa suka kwace a Jihohin Borno da Yobe da gwamnatin Tarayya ta kafa wa dokar ta-baci.

Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun gudanar da taro a birnin Yamai na Nijar domin tattauna barazanar Boko Haram, yayin da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen Yammacin Afirka da tsakiya su gaggauta kafa runduna mai karfi da za ta murkushe kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da zama barazana ga Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.