Nijar

An kange wasu hanyoyin sadarwa na salula a Nijar

Masu zanga-zanga a Yamai
Masu zanga-zanga a Yamai Boureima HAMA / AFP

Kamfanonin sadarwa a Jamhuriyar Nijar tun cikin daren Laraba suka dakatar da bai wa jama’a damar aikewa da sakwanni ta wayoyinsu na Salula da kuma rufe wasu daga cikin hanyoyin sada zumunci irinsu Facebook.

Talla

Duk da cewa babu wasu dalilai da aka bai wa jama’a dangane da haka, amma ana danganta matakin da yiyuwar sake samun tarzoma musamman a gobe juma’a kamar yadda ta faru a makon jiya don nuna kyama ga mujallar Faransa ta Charlie Hebdo.

Musa Changari wani mai fafutukar kare hakkin dan adam, ya ce matakin hana jama’a amfani da hanyoyin sadarwa tauye hakkin jama’a ne.

Changari yace wannan koma-baya ne ga mulkin dimukuradiya da ke son komawa na kama-karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.