DRC Congo

An kashe masu zanga-zanga sama da 42 a Congo

Kikosi cha kusima fujo kikipiga doria  kabla ya kutawanyika waandamanaji si mbali na jengo la Bunge katika mji wa Kinshasa, Januari 19 mwaka 2015.
Kikosi cha kusima fujo kikipiga doria kabla ya kutawanyika waandamanaji si mbali na jengo la Bunge katika mji wa Kinshasa, Januari 19 mwaka 2015. RFI/LL.Westerhoff

Akalla mutane 42 ne aka kashe a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a wata zanga-zangar kyamar ‘yan Majalisa, kan matakin tabbatar da shugaba Joseph Kabila kan Karagar mulkin kasar

Talla

Wata hukumar kula da kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta ce hakan ya auku ne sakamakon karfin da Jami’an tsaro suka yi amfani da shi da kuma ya wuce kima, ga masu zanga-zanga.

Gwamnatin kasar dai ta ce mutane 11 ne aka kashe, a yayin da aka kama wasu masu wauwurar Dukiyar jama’a.

Shugaban mabiya darikar Katolika ta Kiristoci a Janhuriyar Demokradiyar Congo Cardinal Laurent Mosengwo Pasinya ya goyi bayan matasan da ke zanga-zanga a kasar, dan ganin an gudanar da zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Pasinya ya soki duk wani yunkuri na sauya kundin tsarin mulkin, abinda ya haifar da zanga-zanga, wadda kungiyoyin fararen hula suka ce yanzu haka an kashe mutane 42.

Jakadiyar kasar Amurka ta musamman Russ Feingold ta bukaci kwantar da hankali a kasar a hirar sa da Rediyo Faransa.

Ta ce sun yi tir da wannan aika-aika da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, kuma suna kira akan a dakatar da kisan.

Shaidun gani da Ido na cewar an ji karar harebe-harbe da suka barke tsakanin ‘yan Sanda da Dalibai masu zanga-zanga da ke cewa Kabila ya sauka daga Ofishinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.