Tanzania-Burundi

Majalisar dunkin Duniya ta gargadi Burundi kan adalci a zabe

Rassemblement à Bujumbura en faveur de la liberté de la presse, et en soutien aux victimes du terrorisme en France, le 11 janvier 2015
Rassemblement à Bujumbura en faveur de la liberté de la presse, et en soutien aux victimes du terrorisme en France, le 11 janvier 2015 Esdras Ndikumana / RFI

Majalisar dunkin Duniya ta gargadi kasar Burundi da ta tabbatar da an gudanar da karbaben zaben da jama’a zasu amince da shi a cikin wanna shekara

Talla

Yanzu haka gwamnatin kasar na tuhumar ‘yan adawa da dama da ke shirin shiga zaben, abinda ake ganin kamar bita-da-kullin Siyasa ne.

Mataimakin Sakatare Janar Jeffrey Feltman ya ce ‘yan kasar Burundi daga kowacce jam’iyya na da hurumin shiga zaben, don a dama da su.

Mataimakin Sakataren ya ce, shirya karbabben zabe na daga cikin muhimman kalubalen da kasar ta Burundi ke fuskanta, kuma wajibi ne a bar ‘yan kasar duka, ba tare da la’akari da banbancin Siyasa.

Har ya zuwa yanzu dai kasar ta Burundi na fama da komadar tattalin arziki da ya samo asali daga Yakin da aka kwashe shekaru 13 da ya yi sanadin kafuwar kasar a shekarar 2006.

Amma ko a zaben da aka yi na shekarar 2010, ya samu kauracewar ‘yan adawa, abinda ya nun acewar har yanzu akwai sauran Rina a Kaba, dangane da batun kafa gwamnatin hadin kan kasa a Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.