Najeriya

Mun bayar da shawarar a dage zabe-Dasuki

Sambo Dasuki mai ba Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha'anin tsaro
Sambo Dasuki mai ba Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha'anin tsaro vanguard

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro Sambo Dasuki, yace sun ba hukumar Zaben kasar shawara ta dage zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu. Dasuki ya fadi haka ne a lokacin da ye jawabi a wani taro a London.

Talla

Dasuki yace akwai matsaloli da dama, da zai sa a jinkirta zaben domin  mutane sama da miliyan 30 ba su karbi katin zabe na dindin ba.

Haka kuma Dasuki yace saboda matsalolli na tsaro ya ba hukumar zabe shawara ta dage zabe da za a gudanar a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Dasuki, wanda ke gabatar da jawabi a gaban mahalarta wani taro da cibiyar Chatham House da ke birnin London na Birtaniya ta shirya, ya yi watsi da bayanan da ke cewa sojojin kasar ba su da kayan fada, yana mai cewa akwai ragwaye ne a cikinsu.

Dasuki yace akwai ragwaye a cikin rundunar sojan kasar, dalilan da suka sa kungiyar Boko Haram ke samun nasara akan dakarun kasar.

Mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan sha’anin tsaro ya ce matakin da kasashen makwabta suka dauka na canza wa cibiyar rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin zuwa kasar Chadi ba abin da zai canza domin kuwa bai ga amfanin hakan ba a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.