Saudiya

Sarki Abdullah na Saudiyya ya rasu

Sarki Abdullah bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiyya
Sarki Abdullah bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiyya AFP PHOTO/POOL/BRENDAN SMIALOWSKI

Sarkin kasar Saudiyya Abdullah ben Abdul Aziz ya rasu a cikin daren da ya gabata yana shekaru 90 a duniya, kuma tuni aka nada yarima mai jiran gado Salman Ben Abdul Aziz a matsayin sabon sarkin kasar.

Talla

Da misalin karfe daya na daren jiya ne agogon kasar ta Saudiyya fadar sarkin da ke birnin Riyad ta sanar da mutuwar Abdullah Ben Abdul Aziz bayan da aka kwantar da shi a asibitin tun a ranar 31 ga watan disambar da ya gabata.

A yanzu dai an nada yarima mai jiran gado Salman ben abdul aziz mai shekaru 79 a duniya wanda kuma dan uwa ne ga Abdullah a matsayin sabon sarki.
Marigayi Abdullah ya dare kan karagar mulki ne a shekara ta 2005, to sai dai a cikin ‘yan shekarun baya bayan nan an kwantar da shi sau da dama a asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

A sanarwar da ta fitar jim kadan bayan da aka sanar da mutuwar sarkin, fadar shugaban Amurka Barack Obama ta bayyana Abdullah a matsayin wanda ya taka gagarumar rawa wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, yayin da shugaba Francois Hollande na Faransa ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Wani lokaci a yau ne dai za a a yi jana’izar marigayin Abdullah a birnin Riyad yayin da tuni aka soma juyayi dangane da mutuwarsa a duk fadin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.