Sierra Leone

Za a sake buda makarantun kasar Saliyo

Jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Freetown Sierra Leone
Jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Freetown Sierra Leone © Reuters

Hukumomin kasar Saliyo sun bayyana aniyarsu ta dakatar da bai wa jami’an kiwon lafiyar kasar kudaden alawus da aka soma bayarwa domin karfafa masu gwiwa wajen fada da cutar Ebola a kasar.

Talla

Hukumomin sun ce daga karshen watan Maris za a dakatar da biyan kudaden, da suka kai Euro 120 a kowane mako, ga kowane jami’in kiwon lafiya 1, baya ga albashinsa.

Har ila yau hukumomin na Saliyo sun ce za a sake buda makarantun kasar a cikin watan Maris mai zuwa lura da yadda cutar ta soma ja da baya.

Daga cikin mutane sama da dubu 9 da suka mutu sakamakon kamuwa da Ebola, dubu 3 'yan asalin kasar Sierra Leone ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.