Zambia

An rantsar da Lungu a Zambia

Edgar Lungu sabon shugaban Zambia
Edgar Lungu sabon shugaban Zambia AFP PHOTO / CHIBALA ZULU

An rantsar da Edgar Lungu a matsayin sabon shugaban kasar Zambia wanda ya gaji marigayi Michael Sata. Egdar Lungu ya zamo shugaban kasar Zambia na 6 bayan ya gaji marigayi Michael Sata.

Talla

Lungu ya rike mukamai biyu a lokacin gwamanatin Michael Sata da suka hada da ministan shari’a da kuma ministan tsaro. Kuma ya kasance shugaban jam’iyyar PF da ta tsayar da shi a matsayin dan takararta a wannan zaben da ya lashe.

An haifi Edgar Lungu a ranar 11 ga watan Nuwamban shekara ta 1956 a Chadiza da ke lardin gabashin kasar.

Bayan ya kammala karatun lauya a jami’ar Zambia, a shekara ta 1981, ya shiga cikin tawagar rundunar sojin kasar, inda ya samu horo

Daga bisani, Edgar Lungu ya shiga siyasa inda ya fara da jam’iyyar UPND karkashin jagorancin Anderson Mazoka amma bayan wani lokaci, ya canza sheka zuwa jam’iyyar PF da marigayi Michael Sata ya kafa.

A lokacin da PF ta lashe zaben 2011, Edgar Lungu ya samu mukamin karamin minista yayin da daga baya, a aka ba shi ministan cikin gida a ranar 9 ga watan yulin shekara ta 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.