Najeriya

Sojoji sun kori Boko Haram a Maiduguri

Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram RFI/Nicolas Champeaux

Sojojin Najeriya sun fatattaki Mayakan Boko Haram wadanda suka kaddamar da farmaki domin kwace Maiduguri babban birnin Jihar Borno bayan Mayakan sun kwace Mungono tare da kai farmaki a Konduga a karshen mako.

Talla

Wani Mazauni garin Maiduguri ya ce komi ya lafa a garin bayan musayar wuta da aka yi tsakanin hadin guiwar Sojoji da ‘yan kato da gora da Boko Haram.

Rundunar Sojin Najeriya tace Mayakan Boko Haram da dama ne aka kashe a yayin da Sojoji ke musayar wuta da su domin kwato Konduga tare da hana su shiga Maiduguri.

Wata majiya ta tabbatar wa RFI hausa cewa Mayakan na Boko Haram sun kwace wani barikin Sojoji a Munguno garin da ke kusa da Maiduguri.

Rahotanni sun ce daruruwan mutanen garin Mungonu ne ke gudun hijira bayan garin ya fada hannun Boko Haram, wadanda suka shiga suna kashe Mutane da kone konen gidaje.

Tuni dai rundunar sojin ta Najeriya ta kafa dokar hana fita ta sa’o’I 24 a Maiduguri bayan kai harin a ranar Litinin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.