Masar

An cafke ‘yan uwa musulmi 500 a Masar

Daliban Jami'a suna zanga-zanga a birnin Al Kahira
Daliban Jami'a suna zanga-zanga a birnin Al Kahira Reuters/路透社

Hukumomi a kasar Masar sun bayyana kama fiye da ‘yan Uwa Musulmi 500 masu zanga-zanga, bayan da wata arangama ta barke tsakaninsu da jami’an tsaro. Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake zanga-zangar tunawa da cika shekaru 4 da kifar da gwamnatin tsohon shugaba Husni Mubarak. Masu zanga-zangar suna yin allahwadai ne da gwamnatin Abdelfatah al-Sisi akan yanda gwamnatin ke tafiyar da shugabanci a kasar.

Talla

A kwanan nan kotu ta wanke ‘yayan Hosni Mubarak da ake zargi sun wawuri kudaden al’umma a zamanin mulkin Mahaifinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.