Ebola

Liberia ta yi ikirarin kawo karshen Ebola a Fabrairu

Cibiyar kula da majinyatan Ebola a Liberia
Cibiyar kula da majinyatan Ebola a Liberia ©REUTERS/Baz Ratner

Kasar Liberia da ke fama da Cutar Ebola tace za ta kawo karshan cutar kafin karshen watan gobe kamar yadda wani Ministan kasar ya sanar a wata ganawar da ya yi da manema labarai a Geneva.

Talla

Sabon alkaluma da aka fitar na cewar an samu raguwar mutane da ke dauke da cutar zuwa 5 a sati ba kamar yadda a baya ake samun kusan mutane 300 a duk sati dauke da cutar musamma a cikin watanin Agusta da satumba shekarar da ta gabata ba.

A lokacin ganawar sa da yan jaridu a Geneva ministan kasuwanci na Liberia Alex Addy ya ce kafin watan fabrairu suna da tabbacin cewa za a dai na samun mutane da ke kamuwa da cutar Ebola.

Yace akwai tsaurara matakai da suka dauka a iyakokin kasar don tabbatar da cewa ba a samu yaduwar cutar ba.

Rahotani dai na cewa samun tallafin kasahen wajen da kuma yadda ake aikewa da jami’an kiwo lafiya a kasar ya sa an samu nasara wajen yaki da yaduwar cutar

Sabbin alkalumman hukumar lafiya ta duniya na cewa mutane dubu takwas da dari shida da tamanin da takwas ne suka mutu cikin mutune 21,758 da suka kamu da cutar tun bulluwarta a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.